fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Yan sanda sun cafke wasu mutane 40 da ake zargin da satar mutane a Jihar Adamawa

Rundunar yan sanda reshen Jihar Adamawa sun damke wasu mutane 40 da ake zargi da hannu a satar shanu, satar mutane da kuma kisan kai da gangan.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda ta jihar da ke Yola a ranar Litinin, Kwamishinan‘ yan sanda na jihar, CP Aliyu Adamu, ya ce rundunarsa tare da hadin gwiwar mafarautan yankin, sun samu wannan nasarori ne a yayin gudanar da ayyukan a fadin jihar.

Ya bayyana cewa biyar daga cikin wadanda ake zargin suna cikin kungiyar asiri da ke ci gaba da ayyukan satar mutane a fadin kananan hukumomin Yola North, Yola South, Fufore, da Mayo Belwa, kuma a ci gaba da bincike, an gano cewa biyar din su ne wadanda suka sace Hakimin Mayo- Farang a karamar hukumar Mayo-Belwa a watan da ya gabata.

Ya ce an kwato bindigogi kirar AK47 guda uku, mota daya kirar Sharon, da kuma kudi kimanin miliyan N1.1 daga hannun su.

Kwamishinan ‘yan sandan ya kara da cewa biyu daga cikin wadanda ake zargin, su ne Ali Dankaru, mai shekaru 37; da Ahmadu Dajo, su shi mai yana da shekaru 37; sun hada baki tare da wasu mutum hudu tare da yin garkuwa da wani Muhammadu Zakari na Nasarawo Jereng a karamar hukumar Mayo-Belwa, inda suka karbi N550,000 daga iyalansa, suka nemi a ba su kudin fansa har na Naira miliyan 5 in da sharadin iyalan za su biya wannan zuwa ranar kasuwar Nasarawo ta gaba, idan basu so a kashe shi.

Kwamishinan ya ce, sun gano hakan, kuma suka yi bincike mai kyau sannan suka kama wadanda ake zargin. Ya kara da cewa zasu zurfafa bincike a kafin su tura su gurfanar da su a gaban kotu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *