fbpx
Monday, March 1
Shadow

Yan sanda sun cafke wasu mutane uku da ake zargin dillalan makamai ne a Birnin kebbi

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kebbi ta ce ta cafke wasu mutane uku da ake zargin dillalan makamai ne a cikin jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, DSP Nafi’u Abubakar, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Birnin Kebbi a ranar Litinin.
NAN ta ruwaito cewa Abubakar ya kuma bayyana cewa rundunar ta kama wani shahararren mai satar mutane da ke haifar da ta’addanci a jihar.
A cewarsa, duk masu laifin da aka kama za a gurfanar da su a kotu da zarar an gama bincike.
“‘ Yan sanda da ke aiki a Hedikwatar ’Yan sanda na shiyya, Birnin Yauri, sun cafke wani mutum mai suna Ibrahim Bulus, dan shekara 25, saboda mallakar bindigogi uku da ake kerawa a cikin gida da kuma wata karamar bindiga guda daya.
“Lokacin da aka tambaye shi, ba zai iya bayar da gamsassun bayanai game da bindigogin ba.
“Sai dai ya bayyana cewa wasu mutane biyu ne suka ba shi kwangilar ya ba da makaman da aka samu a hannun sa.
“Bayan da aka samu bayanai masu yawa daga wajen sa, nan take jami’an suka ci gaba da cafke masu laifin biyu, wadanda suke zaune a gida daya tare da shi, Ayuba Bulus mai shekaru 42 da kuma Usman Musa mai shekaru 40.
“Har ila yau, wani Salihu Liman, 27, na garin Kangiwa, wanda ya yi zargin ya sace wani Salihu Abdullahi, mai shekaru 26 a gidansa kuma an kama shi.
“Ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu da zarar sun kammala,” inji shi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *