fbpx
Friday, February 26
Shadow

Yan sanda sun cafke wasu yan fashi da makami 9 da ke addabar al’ummar Abuja, tare da kwato makamai

Rundunar ‘yan sanda ta FCT ta kama mutum tara (9) dauke da muggan makamai masu firgita mazauna garin da masu amfani da hanya a kan hanyar Jabi-Utako, Wuse da Kwali.
Wata sanarwa da ASP Yusuf Mariam, kakakin rundunar ‘yan sanda na FCT Command ta ce an kama wadanda ake zargin a yayin gudanar da ayyukan leken asiri daban-daban tsakanin ranakun 10 zuwa 18 ga Fabrairu, 2021.
Wadanda ake zargin sune: Adah Johnson 20, Ebere Ekueme 19, Freedom Emmanuel 20, Gambo Alanana 19, Gideon Adaga 35, Friday Adanu 20, Danjuma Gambo 19, Abubakar Aliyu 20 da Jude Godwin 25 duk maza.
Kayan da aka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da: karamar bindiga guda uku (3), harsashi guda hudu (4), adda guda (1), wuka guda 1, talabijin uku (3) wayoyin hannu, (4) da kuma kudi naira dubu dari da talatin.
Za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike. “Muna yin kira ga mazauna garin da su kwantar da hankulansu, masu bin doka da oda tare da sake jaddada aniyarmu ta kare rayuka da dukiyoyi a cikin babban birnin tarayya”.
“Rundunar tana umartar mazauna yankin da su kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da su ba, na gaggawa ko na damuwa, ta wadannan lambobin: 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883 kuma su kawo rahoton halin da jami’an ‘yan sanda ke ciki, sai a kira layin Ofishin korafin Jama’a (PCB): 09022222352

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *