Rundunar ‘yan sanda ta babban birnin tarayya, FCT, ta samu nasarar cafke mambobin kungiyar yan Shi’a, wadanda ke shirin afkawa’ yan kasa da lalata dukiyar jama’a.
Jami’ar hulda da jama’a tta rundunar ‘yan sandan Abuja, Mariam Yusuf ta sanar da kamun a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
Misis Yusuf ta ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike.