fbpx
Saturday, May 28
Shadow

Yan sanda sun ceto mutane 15 da aka yi kokarin safarar su a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta kama wasu gungun masu safarar mutane da ke tafiya kasar Libya ta kan iyakar Jamhuriyar Nijar.

‘Yan sanda sun ceto mutane 15 da suka hada da mata takwas da maza bakwai da misalin karfe 03:30 na safiyar Juma’a 8 ga Afrilu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, a wata zantawa da manema labarai a hedikwatar rundunar, Katsina, ya ce an kama su ne a baraji Quarters dake karamar hukumar Daura a jihar yayin da suke kai wadanda abin ya shafa.

Karanta wannan  'Yan Bindiga sun kashe Delegates 3 a jihar Naija

Rahotanni sun ce direban ya watsar da wadanda lamarin ya rutsa da su ya kuma garzaya cikin daji bayan ya ga ‘yan sanda. Ana ci gaba da kokarin cafke wadanda ake zargin da suka gudu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.