fbpx
Saturday, June 10
Shadow

Yan sanda sun ceto mutum 5, sun kashe ɗan fashi a Kaduna

Jami’an tsaro a Jihar Kaduna sun yi nasarar ceto mutum biyar da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin Birnin Gwari.

Kwamishinan Tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya ce lamarin ya faru ne da tsakar ranar Juma’a bayan dakaru sun samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga sun tare hanyar Birnin Gewari zuwa Kaduna.

A cewar kwamishinan, nan take jami’an tsaro suka isa kuma suka yi nasarar tserar da mutanen bayan fafatwa da ‘yan fashin.

A wata fafatawar ta daban, jami’an sun kashe ɗan fashi ɗaya tare da kama wani bayan sun buɗe wa motar ‘yan sanda wuta.

Aruwan ya ce bincike ya nuna cewa mutanen suna ɗauke ne da makamai domin kai wa ‘yan fashin daji a Zamfara da Katsina da Kaduna da Neja.

Kazalika, rundunar jami’an tsaron haɗin gwiwa ta yi nasarar ƙwato shanu 32 da tumakai 10, waɗanda ‘yan bindigar suka sace a Ƙaramar Hukumar Kachia.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *