Jam’an ‘yan sanda sun ceto wani jariri sabuwar haihuwa da aka ya sar dashi a nannade a cikin zani a wani kwalbati da ke yankin Abuja Estate a Awka, babban birnin jihar Anambra, in ji kakakin‘ yan sanda Haruna Mohammed a wata sanarwa da ya fitar a jiya.
Mohammed ya bayyana cewa, duk kokarin da aka yi don gano mahaifiyar jaririn amma hakan ya ci tura.
A cewar sa, bayan rahoton da Jami’an ‘yan sanda su ka samu, sun ziyarci wurin inda su kai nasarar ceto jaririn, wanda ke cikin koshin lafiya,” in ji shi.
A ranar 3 ga Oktoba ne Wani mazauni a yankin Awka ya bada rahoto a ofishin ‘yan sanda dake a yankin game da jaririn da aka yasar.
Muhammad kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da cewa, tuni rundunar ta kai jaririn zuwa Asbitin kula da yara wanda daga bisani rundunar zata mika yaron gidan Rainon yara.