fbpx
Thursday, July 7
Shadow

Yan sanda sun dakile yunkurin sace mutane a hanyar Kaduna zuwa Abuja

ASP Muhammad Jalige, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar a ranar Laraba, ya bayyana cewa, a ranar Laraba 9 ga watan Nuwamba da misalin karfe 7.45 na rana, kwamishinan ‘yan sandan, Mista Mudassiru Abdullahi, ya kai ziyarar aiki a hukumance, inda ya tare wasu gungun ‘yan fashi da makami.

Ya ce, “Kwamishinan ya kama wasu gungun ‘yan fashi da makami a wani mummunan aiki a kusa da sansanin Alheri.

“Ya jagoranci jami’ansa suka fatattaki ‘yan fashin zuwa cikin dajin da dabarar harbin bindiga a sakamakon haka, sun tsere da raunukan harsashi.”

Karanta wannan  Ahir dinka, karka kara dangantamu da Peter Obi, Haramtacciyar kungiyar IPOB ta gargadi Kwankwaso

Jalige ya kara da cewa, CP Abdullahi ya umarci jami’an da ke kula da ’yan fashi daban-daban a kan babbar hanyar da su kasance mararsa tausayi ga ‘yan bindiga domin sauya martabar tsaro a hanyar.

Jalige ya ce, “CP ya kuma yi kira ga al’ummomin da ke makwabtaka da su da su kai rahoton duk wanda aka samu da raunin harbin bindiga ga rundunar ‘yan sanda mafi kusa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.