Hukumar ‘yan sandan Najeriya sun cafke dan bindiga a jihar Kaduna inda suka kwace bindigar AK47 a hannunsa.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalinge ne ya tabbatar da wannan labarin ranar asabar.
Inda yace sun samu labari ne akan ‘yan ta’addan sai suka kai masu hari suka damke daya suka kwace bindigar AK47 a hannunsa a Saminaka dake karamar hukumar Lere a jihar Kaduna.