fbpx
Friday, August 12
Shadow

‘Yan sanda sun damke mutumin daya fille kan yaronsa da zarto a jihar Delta

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta damke Volt Blessing Gabriel bayan ya kashe yaronsa dan shekara daya da haihuwa a jihar Delta, Godspower Gabriel.

Mai magana da yawun hukumar ta jihar Delta, Bright Edfe ne ya bayyana wannan labarin, inda yace sun damke mutumin ne ranar alhamis din data gabata.

Inda ya kara da cewa matarsa Mrs. Success Oduwa ce ta kawo karansa ofishin hukumar, sai yace masu fille kan yaron yayi da zarto a cikin jeje sai ya jefar da gangar jikin ya binne kan.

Leave a Reply

Your email address will not be published.