fbpx
Friday, December 2
Shadow

‘Yan sanda sun gano gidan sayar da jarirai a Nasarawa

Rundunar ‘yan sanda Nasarawa da ke Najeriya ta ce ta gano gidan da ake zargin sayar da jarirai a karamar hukumar Karu na jihar.

Rundunar ta ce ta ceto mata shida da kuma jariri ɗan wata shida a gidan.

A sanarwar da suka fitar, jami’in hulda da jama’a na yansanda yankin, DSP Ramhan Nansel ya ce da misalin 2 na rana suka kai samame Karu bayan samun wasu bayanan sirri.

Ya ce ana basaja da gidan ne a matsayin gidan kula da marayu. Sai dai bincike ya gano cewa ana garkuwa da kananan yara ana yi musu ciki sannan a sayar da jariran da suka haifa.

Karanta wannan  YANZU-YANZU: Gobara Ta Tashi A Dakin Kwanan Dalibai A Jami'ar Dan Fodiyo Dake Sokoto

An dai cafke wasu mutum uku da ake zargin ke aikata wannan muggun aika-aika.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *