fbpx
Thursday, July 7
Shadow

‘Yan Sanda Sun Gayyaci Sheik Sani Khalifa Zaria Bayan Ya Jagoranci Sallar Idi

Duk da cewa Malamin ya bi umarnin da gwamnati ta bayar na cewa kowa ya yi sallah a gida, amma kasancewar Malamin yana da almajirai da iyalai da dama hakan ya sa jama’a sun samu halartar sallar duk da cewa a gidansa dake Zaria aka gudanar da sallar.

 

Rahotanni sun tabbatar da cewa bayan idar da sallar ne sai ga jami’an ‘yan sanda sun dira gidan malamin, inda suka ce masa ana gayyatarsa zuwa ofishinsu.

 

 

Saidai wasu daga cikin wadanda suka halarci sallan sun fusata, inda suka ki yarda a tafi da Malamin daga bisani aka fitar da malamin ta barauniyar hanya domin ya je amsa gayyarar da ‘yan sandan suka yi masa.

Karanta wannan  Mutanen kauyukan dake kusa da inda aka kaiwa tawagar motocin shugaba Buhari hari sunce tawagar Buharin basu yi musayar wuta da 'yan Bindigar ba, ta kansu suka yi

 

 

Saidai a yayin da ‘yan sandan suka zo, Sheik Sani Khalifa ya tambaye su ko an turo su ne su kama shi, sai suka ba shi amsa da cewa ai ya fi karfin su saka shi a mota su tafi da shi saidai ya zo da kansa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.