fbpx
Thursday, August 18
Shadow

‘Yan sanda sun gudanar da gasar kwallon kafa domin kulla Alaka da fararen hula a Kano

An bayyana wasanni a matsayin manyan abubuwan da ke wanzar da zaman lafiya da hadin kai gami da samar da martabar ga kasa.

Kwamandan kungiyar MOPOL 9, ACP Shuaibu Bello shine ya bayyana hakan a yayin bude gasar kallon kafa da aka shirya a filin wasa na Kano MOPOL.

ACP Bello ya ci gaba da cewa baya ga wannan, wasanni suna kuma taimakawa wajen hada kan kabilu daban-daban tare da kara kulla kyakkyawar dangantaka da juna.

Ya kara da cewa gasar za ta bayar da gudummawa wajen karfafa dankon zumunci tsakanin ‘yan sanda da al’ummar jihar kano musamman al’ummar dake zaune a yankunan.

Da yake jawabi, wanda ya dauki nauyin gasar, Auwalu Idris, ya ce ya yanke shawarar daukar nauyin gasar ne domin bada gudummawa wajan karfafa dankon zumunci tsakanin ‘yan sanda da al’umma.

Rahotanni na nuni da cewa, a kalla kungiyoyin kwallon kafa goma ne za su buga wassani a gasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.