Yan sanda sun kama ‘ƙwararren ɓarawon akuya’ a Kaduna
Kaduna Police CommandCopyright: Kaduna Police Command
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta ce ta kama wani matashi da take zargi “ya ƙware” a satar akuyoyi a ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar.
Kakakin rundunar, ASP Mansur Hassan, ya faɗa wa kamfanin labarai na Najeriya NAN cewa sun kama mutumin ne a ranar Asabar a ƙauyen Pasali Konu.
A cewarsa, matashin mai shekara 20 ɗan asalin ƙauyen Igwa ne kuma an kama shi “ɗauke da makamai masu haɗari da kuma takunkumi a fuskarsa”.
“Wanda ake zargin ya amsa laifinsa cewa su biyu ne suka je ƙuyen don satar akuyoyi,” a cewar ASP Hassan.
Ya ƙara da cewa wanda suke tare da matashin da ake zargin ya tsere bayan ya hangi dakarun ‘yan sanda, amma suna ci gaba da neman sa.