fbpx
Sunday, December 4
Shadow

Yan sanda sun kama dillalin miyagun kwayoyi a Kano, sun kwato sunkin 250 na tabar wiwi wanda kudinsu ya haura N1.7m

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kano sun kama wani dillalin magunguna tare da kwato sunki 250 na tabar wiwi wanda kudinsu ya haura N1.7m.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Juma’a, 15 ga watan Afrilu, ya ce wanda ake zargin, Agbo Victor, ya amsa cewa ya dauko tabar wiwin ne daga jihar Edo zuwa Kano.

A halin da ake ciki, Kwamishinan ‘yan sandan ya bayar da umarnin mayar da shari’ar zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar, sashin binciken miyagun kwayoyi domin gudanar da bincike mai zurfi. Za a gurfanar da wanda ake zargin zuwa kotu bayan an kammala bincike.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *