fbpx
Wednesday, June 29
Shadow

Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da makami a wani artabu da suka yi a jihar Delta, sun kashe mutane 10

Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Delta sun kashe wasu mutane goma da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma ‘yan fashi da makami a wani samame da suka kai a wata maboyar ‘yan ta’adda a yankin Kwale da ke jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Bright Edafe, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 22 ga watan Mayu, ya ce rundunar hadin gwiwa da ta hada da rundunar yaki da satar mutane ta jihar, da kungiyoyin sa kai na Dragon, da jami’an RRS ne suka gudanar da aikin.

Karanta wannan  An yiwa mata fyade tare da 'yarta a motar da suka hau don a rage masu hanya zuwa gida

Kwamishinan yan sandan jihar, ya tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar za ta ci gaba da yakar ta’addaanci a jihar, ya kuma bukaci jama’a, ’yan banga da sauransu, da su ci gaba da hada kai da ‘yan sanda da domin tabbatar da cewa jihar Delta ba ta zama mafaka ga yan ta’adda ba. ta’allaka ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.