Jami’an ‘yan sanda da ke aiki a ofishin leken asiri na jihar (SIB) na rundunar’ yan sandan jihar Adamawa sun cafke mutane uku bisa zargin cire fankoki 120 daga makarantun gwamnati.
Rundunar ta ce an dauki fankokim ne daga makarantu da ke Askira Uba ta Adamawa.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) a jihar Adamawa, Suleiman Nguroje, ya bayyana sunayen mutanen uku a cikin wata sanarwa ga manema labarai a Yola.
Wadanda ake zargin sune Tanko Jessay, dan shekara 23, Linus Waba, 24 da Ahmed Aliyu 23, dukkansu mazauna Njuwa na Askira-Uba.
Sanarwar ta ce yaran sun shiga makarantun kuma sun sace fankokin 120 kuma an kamasu yayin da suke kai kayayyakin jihar Taraba.