A ranar Alhamis din da ta gabata ne rundunar ‘yan sanda reshen jihar Katsina ta ce ta kama mutane uku a wani faifan bidiyo a kafafen sada zumunta da ake zargi da cin mutuncin Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar, Aminu Masari.
Wadanda aka kama din sune; wani mutum dan shekara 70, Lawal Abdullahi Izala; Bahajaje Abu da Hamza Abubakar dukkansu na zaune a Gafai Quarters, a cikin garin Katsina.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya ce, an jawo hankalin rundunar‘ yan sanda ta jihar Katsina ne ta wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna wani Lawal Adullahi, wanda ake kira “IZALA” wanda ke zagin Shugaban Kasa Buhari da gwamna Masari.
Saboda haka, Kwamishinan ‘yan sanda, CP Sanusi Buba, ya ba da umarnin gudanar da bincike wanda hakan ya sanya aka cafke su.in ji shi
Ya kara da cewa a yayin gudanar da bincike, “wadanda ake zargin sun amsa laifinsu ga hukumar.
SP Isah ya kara da cewa, “Don haka, Rundunar ta yi gargadi ga sauran jama’a cewa ‘yan sanda ba za su nade hannu ba, ko su zuba ido ana karya doka ba.