Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Abia ta tabbatar da kama wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a sace wani da a ke kira da Chekwas Daniel dake jihar Aba.
Rundunar ta fitar da sunan Wadanda ake zargi da suka hada da Bright Chinonso, Eze Ernest, Chisom Godwin da Chinoyerem Chineye, wadanda suka yi garkuwa tare da sace wani mutum dake cikin shagon sa a ranar Talata.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Janet Agbede ne, ya tabbatar da kamun masu laifin a Umuahia, a ranar Juma’a.
A cewar sa bayan hukumar ta kammala bincikenta zata gurfanar da wadanda ake zargi a kotu, domin su fuskanci hukuncin abun da suka aikata.
Tun dai da fari Lamarin ya farune a lokacin da masu satar mutanan suka hangi, Nambar mai shagon rubuce a jikin kofar shagun nashi, sai suka, kira Numbar a lakacin mai shagon yaje coci, inda suka bayyana masa suna bukatar sayan Yadi na kudi mai yawa.
Bayan jin hakan yasa mutumin ya dawo shagon da sauri Dan ya hadu da mutanan inda bayan ya dawo sai ya kirasu a waya cewar yanzu ya dawo shagun nasa.
Aikuwa da zuwan su sai suka turashi cikin motarsu da karfin tsiya. Inda sukai garkuwa dashi.