Rundunar ‘yan sandan Imo ta kama wani da ake zargin dan kungiyar yan asalin yankin Biafra (IPOB)/Eastern Security Network ne dake kera bam a wani samame da suka kai a Uba Umuaka da ke karamar hukumar Njaba a jihar.
An kama wanda ake zargin mai shekaru 50, Simeon Onigbo a ranar Alhamis.
Da yake tabbatar da kamun a ranar Juma’a, Kakakin ‘yan sandan, CSP Michael Abattam, ya ce wanda ake zargin da aka yi masa tambayoyi a nan take, ya amince da cewa shi ne ya kera mafi yawan na’urorin abubuwan fashewar da ake amfani da su wajen kai hare-hare ga ofisoshin ‘yan sanda a jihar da kuma wajen ofishin ‘yan sandan jihar
A kakakin: “Ana ci gaba da gudanar da bincike kuma wanda ake zargin ya yi bayani mai amfani kuma ya ambaci wasu ’yan kungiyarsa da ke wajen jihar wadanda suke taimaka masa.