fbpx
Thursday, May 19
Shadow

Yan sanda sun kama wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane a Nasarawa

An kama wani da ake zargin mai garkuwa da mutane ne kan sace wani makiyayi a karamar hukumar Awe da ke jihar, wanda aka sake shi bayan an biya kudin fansa N10m.

Ibrahim Hassan wanda aka ce shi ne shugaban wata kungiyar masu garkuwa da mutane, ya yi garkuwa da Abubakar Babiri dan shekara 23 a Rugarsu yayin da yake kiwo.

Bayan kama shi, wanda ake zargin mai shekaru 42 ya amsa laifinsa. Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, ASP Ramhan Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin.

Karanta wannan  Kalli bidiyo waya ta makale a hannun barawo bayan ya sace ta

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Adesina Soyemi ya bayar da umarnin a gudanar da bincike sosai kan lamarin a sashin binciken manyan laifuka na jihar da ke Lafia.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.