fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

‘Yan Sanda Sun Kama Wani Da Ake Zargi Mai Safarar Bindigagogi ne Tare Da Wasu Yan fashi Da Makami a Jihar Zamfara

Yan sanda a jihar Zamfara sun cafke wasu da ake zargin masu safarar bindigogi da‘ yan fashi da makami ne a wurare daban-daban a fadin jihar, kamar yadda kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Abutu Yaro ya bayyana a ranar Juma’a.
Da yake gurfanar da wanda ake zargin a ofishin ‘yan sanda na jihar, Mista Abutu Yaro ya ce, rundunar ta cafke wani mutum mai suna Ibrahim Adamu, wanda aka fi sani da Gado, bayan bayanan sirri sun nuna cewa shi da wani Tsoho dandela na kauyen Kangon Marafa sun kammala shirin sayen bindigar AK 47.
Ya ce sun shirya sayen bindigar ne daga wani barawon da ake kira Dogo Alo da ke zaune a wani daji a karamar hukumar Zurmi da ke jihar.
“Jami’an mu sun sanya tawagar sa-ido wanda hakan ya sa aka samu nasarar cafke daya daga cikin wadanda ake zargin tare da kudi har N1,070,000 da aka nufa domin jigilar.
“A yayin bincike, wanda ake zargin ya amsa cewa ya karbi kudin daga Tsoho Dandela kuma za a kai shi ga Dogo da ke karamar hukumar Zurmi.
Yaro ya kara da cewa, “A daidai wannan lokacin ne, jami’anmu suka kama wani shahararren dan ta’addan nan mai suna Lawal Ibrahim da bindiga AK 47 guda daya da kuma alburusai biyu kuma ana kokarin shawo kan wadanda suka hada kai da shi.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

Leave a Reply

Your email address will not be published.