Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani da ake zargin dillalin jabu da sa maye mai suna Chibezie Onocha a unguwar Sabon Gari da ke jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadi, 17 ga watan Afrilu, ya ce rundunar ‘yan sanda ta Operation Puff Adder ta kama wanda ake zargin a yayin da jami’an leken asiri suka gudanar da sintiri a kan hanyar IBB a Kano.
Kakakin ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin safarar magungunan daga Legas zuwa jihar Kano da Jamhuriyar Nijar.
Kwamishinan ya ba da umarnin zurfafa bincike kafin gurfanar da shi a gaban kotu, haka ma ya bukaci mutanen jihar da su ci gaba da kai rahoton a ofishin yan sanda mafi kusa kuma kada su dauki doka a hannunsu.

