Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa sun kama wani dan kungiyar masu garkuwa da mutane uku da ke addabar wasu kananan hukumomin jihar tare da kwato bindigogin AK-47 guda hudu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, DSP Suleiman Yahaya Nguroje, a wata sanarwa da ya fitar ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 8 ga Afrilu, 2022.
Ya ce kungiyar da ta kware wajen yin garkuwa da mutane ta addabi kananan hukumomin Yola ta Arewa, Yola ta kudu, Girei, Fufore da Song.
Sanarwar ta ce, CP din ya yabawa kwamandan yankin Karewa da jami’an sa kan yadda suka kori tare da kwato wuraren jama’a, ya bukaci dukkanin jami’an ‘yan sanda na Dibision (Dpos) da kwamandojin su na yankin da su kara kaimi wajen ganin an wargaza masu aikata laifuka tare da hana masu aikata laifuka damar sake yaduwa ko’ina a cikin jihar.
