Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Legas ta cafke wasu mutane biyu da aka bayyana sunansu da Ayan Okorie, dan shekara 45 da kuma wani mai suna Usman Ali, mai shekara 21 da haihuwa da ke lamba 51 a titin Ali Balogun, Ijora Oloye dake jihar Legas. ana zargin su ne da yin sojan gona wajan kiran kansu a matsayin jami’an soji da na ‘yan sanda.
Rahotanni sun rawaito cewa An kama wanda ake zargin ne a lokacn da suke sanye da rigar kariya ta rundunar ‘yan sanda da ke sashin Surulere.
Bayan da aka tuhume su sun Amsa laifin da cewa so ba jami’an tsaro ne na Gaskiya ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu yayi tir da masu aiakta makamancin laifin.