Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata laifuka a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, Muhammed Jalige ya fitar, ya ce an kwato bindigogi kirar AK-47 guda biyu tare da akalla harsasai talatin da biyu daga hannun wadanda ake zargin.
Ya kara da cewa jami’an ‘yan sandan da suka yi aiki da sahihan bayanan sirri sun kama daya daga cikin wadanda ake zargin, dan shekara 25 a karamar hukumar Giwa ta jihar yayin da aka kama na biyun a Tudun Wada da ke karamar hukumar Zariya a Kaduna.
Jalige ya kara da cewa rundunar tana neman karin hadin kai daga jama’a a fannin musayar bayanai yayin da rundunar ta ke kokarin rage aikata laifuka a jihar.
