Jami’an hukumar Rapid Response Squad (RRS) na rundunar ‘yan sandan jihar Legas sun kama wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi da makami tare da kwato karamar bindiga da harsashi guda hudu a tashar motar Toyota da ke kusa da Oshodi.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce kamen da aka yi wa ‘yan fashin a kan hanya ya biyo bayan wasu bayyanan sirri da mazauna Legas suka baiwa jami’an RRS da ke sintiri a Ladipo da Oshodi a Talata, 5 ga Afrilu.
A halin da ake ciki, kwamishinan ‘yan sanda, CP Abiodun Alabi ya umurci Kwamandan RRS, CSP Yinka Egbeyemi da ya mika mutanen uku ga rundunar ‘yan sanda ta musamman na CP domin gudanar da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.