Hukumar ‘yan sandan Najeriya na jihar Bauchi ta kama daliban makarantar Polytechnic dake jihar kan sunyi zanga zanga saboda yajin aikin gargadi da makarantar ta fara na kwanaki 12.
Kuma an an samu labari cewa daga bakin wani dalibi cewa hukumar ‘yan sanda ta karya kafafuwan dalibai guda biyu cikin masu yin zanga zangar.
Inda ya kara da cewa sun jiwa wani malaminsu Sanusi ciwo sannan har gida suka riga bin dalibai suna kamo su kan zanga zangar da suka yi.
Amma mai magana da yawun hukumar ta jihar Bauchi, Ahmad Muhammad Wakili yace tabbas an saka jami’ai a makarantar amma bashi da masaniya kan kama dalibai da kuma karyasu da aka yi.