fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Yan sanda sun kashe mutum 1, sun kama 78 daga cikin mambobinmu yayin da suke tafiya Kaduna – Yan Shi’a

Yan Shi’a na Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) sun yi zargin cewa ‘yan sanda sun harbe dan kungiyarsu tare da kame wasu 78 a Zariya da Kaduna a yayin taron tunawa da ranar Kudus da suke yi a duk shekara.

Sun ce a ko da yaushe ana gudanar da Muzaharar Qudus ta Duniya a duk fadin duniya a ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan, kuma a ko da yaushe ana gudanar da ita ne cikin hadin kai da goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta.

Da yake magana a wani taron manema labarai a Kaduna, Engr. Yunusa. Lawal Musa, memba na IMN, ya ce “Taron ya gudana ne a kusan dukkanin kasashen duniya da suka hada da Amurka, Birtaniya, Jamus, Faransa, Australia, Kanada, Ghana, Jamhuriyar Nijar, da kuma a Najeriya. wasu jahohi da dama, ba tare da wata barazana ko hari ba sai a jihar Kaduna (Kaduna da Zaria).

Leave a Reply

Your email address will not be published.