Hukumar ‘yan sanda tayi nasarar kashe wani barawo a karamar hukumar Idimili dake arewacin jihar Anambra ranar talata.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe daya da minti biyar na yamma inda hukumar sukayi cibis da barayin suna kokarin kwacewa mutane kadarorinsu akan titi.
Yayin da barayin da ‘yan sandan suka fara musayar wuta har jami’an suka kashe mutun daya a cikin su suka kwace bindigarsa ta AK47 kafin sauran suka tsere a motarsu ta Hilux farar Toyota mara lamba.