fbpx
Monday, August 15
Shadow

‘Yan sanda sun kashe wani dan haramtacciyar Biafra a jihar Delta

Hukumar ‘yan sadan jihar Delta sunyi nasarar hallaka wani dan haramtacciyar kungiyar Biafra jiya ranar litinin.

Lamarin ya faru ne a wani kwatas na Ogbada dake karamar hukumar Oshimili a jihar ta Delta yayin da hukumar ke kan aikinsu.

Inda ‘yan haramtacciyar kungiyar ta Biafra guda uku suka bude masu wuta kuma hukumar ta fara musayar da wuta dasu har tayi nasar aika daya daga cikinsu barzahu.

Yayin da su kuma sauran guda biyun suka tsere da raunika a jikinsu, inda hukumar ta dakko bindigar mamacin ta AK47 ta tafi da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published.