hukumar ‘yan sanda na musaman dake jihar Kaduna ta kashe ‘yan bindiga guda hudu kuma sun kama wata mata guda dake taimaka masu.
‘Yan sandan sun kashe sune a ranar laraba 15 ga watan yuni kan hanyar Saminaka zuwa Jos inda sukayi cibis dasu a cikin wata bakar motar Sharon.
Kuma da ‘yan bindigar suka lura cewa su jami’an ke bi sai suka fara bude masu wuta, inda jami’an sukayi nasara suka raunana su kafin suka kaisu asibitin Barau Dikko,
Inda suka mutu a asibitin kuma hukumar ta bayyana cewa mutanen sune ke kaiwa ‘yan bindiga makamai.