fbpx
Thursday, February 25
Shadow

Yan sanda sun kwato kudade da makamai daga hannun masu satar mutane a jihar Neja

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Neja ta ce ta gano kudi,  miliyan N3.5 da makamai daga masu satar mutane da ke addabar mazauna yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda na jihar, Abiodun Wasiu, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin lokacin da yake yi wa manema labarai bayani a Minna, babban birnin jihar.
A cewar Wasiu, an kama yayin da jami’an ‘yan sanda da ke sashin yaki da masu satar mutane ke sintiri a kan hanyar Gwada da Shiroro.
Ya ce, “An kama Abdulkareem da Nura tare da kudi miliyan N1.5 a hannunsu. A yayin bincike, wadanda ake zargin sun amsa cewa su ‘yan fashi da makami ne da ke addabar yankin Kasasu da Galadima Koga da ke karamar hukumar Shiroro kuma kudin sun samu ne daga satar mutane da kuma satar shanu. “
Kakakin ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa, rundunar na gudanar da bincike a kan wani da ake zargi da aka kama a kan titin Ibbi / New Busa.
Ya ce an samu wanda ake zargin da miliyan N1.7, ya kara da cewa ya amsa cewa kudin nasa kasonsa ne daga kudin fansa da aka karba daga mutanen da aka sace a yankin Nasko da Mashegu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *