fbpx
Friday, December 2
Shadow

‘Yan sandan DSS kwalaben magani biyu suke ba Nnamdi Kanu a madadin bakwai daya kamata su bashi, cewar luyan IPOB

Lauyan shugaban haramaracciyar IPOB, Ifeanyi Ejiofor ya bayyana cewa hukumar ‘yan sandan DSS dake tsaron shugabansu basa kula da lafiyarsa yadda ya kamata.

Inda ya bayyana cewa hatta maganinsa kwalabe bakwai ne ya kamata ace ana bashi amma su kam basu damu ba kwalabe biyu kacal suke bashi, saboda haka ya kamata su bari iyalansa su kula dashi.

A karshe yace rashin lafiyar shugaban nasa wanda ya kwashe sama da watanni 14 a kurkuku yayi kamari sosai, saboda haka ya kamata su bari ‘yan uwansa au kula da lafiyarsa tunda su ba zasu iya ba.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *