fbpx
Sunday, March 26
Shadow

‘Yan sandan kasar Indiya zasu yi amfani da jirgi marar matuki dan gano masu yin bahaya a waje

A kasar Indiya jihar Telanagana hukumomin sun dauki wani mataki da ba kasafai aka saba jin irinshi ba dan kama masu yin bahaya da fitsari a bainar jama’a, ‘yan sanda ne a jihar zasu yi amfani da fasahar jirginnan marar matuki dan gano duk wani da zaiyi yunkurin yin bahaya ko fitsari a jikin wani sabon Dam da ake ginawa wani gari dan samar musu da ruwa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wannan labari dai ya dauki hankulan mutane, ko da yake ga wadanda ke bibiyar al’amuran kasar Indiya, kasa ta biyu a Duniya mafi yawan mutane, wannan labarin bazai bashi mamaki ba saboda ko da a shekarun baya hukumomi a kasar sun dauki matakai iri-iri dan hana mutanen kasar yin bahaya ko fitsari a waje.

Misali akwai lokacin da hukumomin kasar suka umarci iyayen ‘yan mata kada su aurawa duk wani mutum da baida bandaki agidanshi ‘yarsu, wannan ya farune saboda kokarin da hukumomin suke na rage yawan masu yin bahaya a waje, dan rahotanni sun nuna cewa kusan rabin ‘yan kasar basu da bandaki kuma mutanen kasar sunfi kokarin rike waya akan yin bandaki.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Ban ce ba zan ba Tinubu Mulki ba>>Shugaba Buhari

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *