Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum bakwai da take zargi da safarar makamai a jihohin Taraba da Filato na tsakiyar ƙasar.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yammacin yau Alhamis ta ce ta kama su ne a wani samame da rundunar musamman ta haɗin gwiwa tsakanin FIB da IRT ta kai.
Ta ce ta ƙwace bindigar AK-47 guda 57 daga hannun waɗanda ake zargin. Yayin bincike, wasu daga cikinsu sun faɗa wa ‘yan sanda cewa sun sayi bindigar AK-47 da kuma ƙirar SMG kan kuɗi naira 900,000.
Rundunar ta bayyana sunayensu kamar haka: Hamza Zakari mai shekara 20, Abubakar Muhammed shekara 22, Umar Ibrahim shekara 25, da kuma Muhammed Abdulkarim wanda aka fi sani da Dan-Asabe mai shekara 37.
Sauran su ne: Bello Sani, da Venab Puncat, da Yusuf Nahoda.
‘Yan sanda sun ce suna ci gaba da bincike kan mutanen kafin gurfanar da su a gaban kotu.