fbpx
Thursday, May 26
Shadow

‘Yan Sara-suka Sun Kusa Hallaka Wani Ɗan Sintiri A Katsina

Daga Zaharaddeen Gandu

Wani ɗan sintiri ya tsallake rijiya-da-baya a hannun ‘yan sara-suka waɗanda ake kira da ƙauraye a katsina, lamarin ya faru ne a safiyar jiya labara a cikin sabuwar unguwa, inda suka kusa hallaka wani matashi Sani Maikuɗi.

Saide shugaban haɗaka na ‘yan sintirin sabuwar unguwa, Ibrahim Aliyu D-Mash ya bayyana mana musabbabin abin da ya faru, inda ya bayyana cewa:

“jiya mun fita ne domin mu yi maganin ɓatagari da suke faɗa da ‘yan sintiri masu hanasu sare-sare da fizge wa baƙi waya idan sun shigo sabuwar anguwa kasantuwar Sallah ce baƙi zasu shigo, to munyi ƙoƙari mu daƙile wannan al’amari, muntaho sai wasu mutanenmu su 3 suka tsaya baya bamusan sun tsaya ba, to ashe wasu sun ɓoye a lungu da wuƙaƙe, sai suka hau kansu da sara, ɗayan wuƙa bata kamashi sai suka farma wanda sukaga wuƙa na kamashi suka sareshi a ƙafa da kansa da hannunsa”.

“kowa ya sani da ance sabuwar unguwa to ansan tayi ficce wajen ƙauraye da faɗace-faɗace, domin ko mace kake so baka iya zuwa unguwar taɗi idan kai ba ɗan unguwar ba ne, saide ka samu ɗan unguwar ya rakaka, kamar ni nasha inraka wasu su yi taɗi idan sun gama mutaho tare su tafi anguwarsu, daga ƙarshe kuma wani ya auri wata”.

“saide kuma sabuwar unguwar ta kasu kashi-kashi, saboda unguwar tana da faɗi da yawa, akwai yankin da idan kaje babu wata matsala, akwai kuma yanki idan kaje mahaifan nasu ne ke goya musu baya duk wani ta’addanci na sace-sace da sare-sare na ƙaurancin su suka amince su yi haka, saboda basuso a hukunta yaransu”.

Karanta wannan  EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Rivers, Rochas Okorocha

“daga ƙarshe, muna kira da gwamnati ta taimakemu idan mun kama yaro mun kai wa jami’an tsaro da su daina bada su belin, saboda iyaye na zuwa su saida ƙaddarorinsu su fiddo yaronsu, ko kuma gwamnati ta saida gidansu su tashi su barmana unguwarmu”. Inji Shugaban haɗaka na ‘yan sintirin Sabuwar Unguwa

Har ila-yau, wani Jamilu Ustaz ya shaida mana cewa, “yan sintiri suna ƙoƙari sosai, saide ƙaurayen suna da yawan gaske, wanda adadinsu yakai mutum 400 suka yo ayari domin karɓar wani ƙaura da ‘yan sintirin suka kama, ƙaurayen sun yi wa ‘yan uwansu waya ne shaf-shaf suka unguwar”. Inji shi

A yayin haɗa wannan rahoto, munso jin ta bakin Sani Maikuɗi, wanda aka sara amma wayarsa a kashe, sannan munje har gidansu alokacin ana wanke masa ciwonsa babu damar yin magana da shi.

Daga ƙarshe, dattawan sabuwar unguwa sun ayyana cewa, “muna kira da gwamnati da ta kawo mana ofis ɗin civil defence, irin wanda aka buɗe a kobren ɗorowa, domin kuwa za a samu sauƙi idan akai hakan sosai, domin abin kullum daɗa ƙaruwa yake”, Inji su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.