fbpx
Monday, March 1
Shadow

‘Yan shi’a mabiya Zakzaky sun zargi Gwamnatin Kano da goyon bayan ‘yan ta’adda sun soki hana Abduljabbar Kabara Wa’azi

Kungiyar Shi’a, bangaren Sheikh Ibrahim Zakzaky, IMN ta bayyana cewa tana Allah wadai da hana Sheikh Abduljabbar Kabara wa’azi.

 

A sanarwar da suka fitar sun bayyana cewa gwamnatin Kanon ta dauki hukuncinne ba tare da yin bincike ba.

 

Suka ce gwamnatin ta zagaye kanta da Malaman Sunna wanda suka ce yawanci suna bin koyarwar Ibn Taymiyya ne wanda mafi yawanci  masu kashe mutane da sunan Addinin Musulunci, koyarwarsa suke bi.

 

IMN tace an an yiwa Zakzaky irin wannan hakanan gashi kuma an zo kan Sheikh Abduljabbar Kabara,  sannan an kama daliban Sheikh Dahiru Bauchi a Kaduna, to suma fa abin wataran na iya fadowa kansu.

 

IMN tace tana kira ga gwamnatin jihar Kano data sa a yi muhawara tsakanin malaman da Sheikh Abduljabbar Kabara kuma yana da ‘yancin yin addininsa tunda ba ya tursasa kowa da cewa dole sai ya bishi. Hutudole ya fahimci cewa ‘yan shi’ar sun ce ya kamata a mutunta kundin tsarin mulki da ya baiwa kowa damar yin addininsa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *