Kungiyar ‘yan Shi’a ta nemi hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa data saka baki wajan yiwa gwamnatin tarayya magana a sakarwa Zakzaky takardunsa na Fasfon tafiye-tafiye dana matarsa.
Sun yi Zanga-Zanga a ofishin hukumar kare hakkin bil’adama dake Abuja inda suka zargi gwamnatin tarayya da take hakkin Zakzaky.
Kungiyar tace watanni 9 kenan da sakin Zakzaky da kuma wankeshi daga zarge-zargen da ake masa da kotu tayi.
Amma hukumomin Najeriya sun ki bashi Fasfsonsa dan yaje neman magani da iyalansa a kasar waje.
Wakilin kungiyar ya gayawa manema labarai cewa, sun jira amma gwamnati bata dauki matakin da ya dace ba shiyasa suka dawo yin Zanga-Zanga.