‘Yan shi’a sun gudanar da zanga zangar lumana a babban birnin tarayya Abuja ranar litinin inda suka bukaci a baiwa shugabansu El Zakzaky da matarsa Zewnat fasfo dinsu.
Mabiya shi’ar sun gudanar da zanga zamgar ne akan babbar hanyar Aguyi Ironsi dake Maitama a babban birnin tarayyar inda suka zargi gwamnatin Buhari d tauye hakkin shugaban nasu.
Shekara guda kenan da babbar kotun jihar Kaduna ta wanke Zakzaky akan zarhin da ake yi masa na aikata ta’addanci, amma har yanzu kotun bata bashi fasfo dinsa ba.
Wanda hakan yasa mabiyansa suka bukaci a bashi domin yaje kasar waje nemo lafiya, kuma sunce tunda an hana shi duk abinda ya same to zasu dora laifin akan gwamnatin Buhari.

