Ƙungiyar ‘yan Shi’a a Najeriya ta Islamic Movement in Nigeria ta yi Allah-wadai da zanen barkwanci na ɓatanci da jaridar Charlie Hebdo ta yi wa Annabi Muhammadu SAW.
Jaridar wadda ake bugawa a ƙasar Faransa, ta sake buga zanen barkwancin ne ranar 31 ga watan Agusta kwana ɗaya kafin shari’ar mutanen da suka kai wa gidan jaridar hari tare da kashe mutum 12 sakamakon zanen farko da ta yi na ɓatanci a 2015.
“Mun yi Allah-wadai da zanen na ɓatanci ga Annabi Muhammadu SAW kuma muna kallonsa a matsayin laifi,” IMN ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta aike wa BBC a yau Talata.
Ta ƙara da cewa: “Zanen yana matsayin kalaman ƙiyayya ne kuma zai tunzura Musulmai. Yunƙurin da Shugaban Faransa Macron ya yi na bayyana hakan a matsayin ‘yancin faɗar albarkacin baki ba karɓaɓɓe ba ne.”
Ƙungiyar ta kuma ce babu wayewa a cikin yin zanen ɓatancin sannan kuma ‘yancin faɗar albarkacin baki “bai bai wa mutum damar ya muzguna wa wani ba”.
Ita ma ƙungiyar Izala (JIBWIS) a Najeriya ta buƙaci mamallakin dandalin Facebook ya rufe duk shafin da ya yi ɓatanci ga Annabi SAW.