fbpx
Monday, August 3
Shadow

‘Yan Siyasa na wasa da rayukan mutane a kasarnan>>Gwamna Yahaya Bello

Gwamnan jihar Kogi,Yahaya Bello ya sake ci gaba da jaddada maganarsa ta cewa cutar Coronavirus/COVID-19 ba gaskiya bace, gwamnan ya bayyana hakane a yau Alhamis yayin da wata gidauniyar Sir Ahmadu Bello dake ta kai masa ziyara a gidan gwamnatin jihar Kogi.

 

Yace cutar Coronavirus/COVID-19 ba sabuwa bace a Najeriya, rufe mutanen da ake yi kawai yana kara saka sune cikin wahalar rayuwa da yunwa.

Gwamnan yace maimakon saka mutanen mu cikin wahala, kamata yayi a yi amfani da wannan damar wajan yin abin rufe hanci da baki ana fitar dashi zuwa kasashen waje Najeriya ta samu kudin shiga.

 

Gwamnan ya jaddada cewa ba cutar Coronavirus/COVID-19 bace ta kashe babban alkalin jihar Nasir Ajana ba.

 

Yace ya sanshi sosai dan uwansane inda yace tun shekarar 2016 yake fama da rashin lafiya amma yanzu aka killace shi aka hanashi ganawa da kowa har sai da ya mutu. Yace ya kamata a daina wasa da rayukan mutane haka.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *