Akwai ‘yan siyasar Najeriya 3 da suke da miliyoyin mabiya a shafukan sada zumunta amma kuma duk sun fadi zabukan fidda gwani a mazabunsu da suka tsaya takara.
Na farko shine Sanata Dino Melaye;
Sanata Melaye na da mabiya Miliyan 3.3 a shafinsa na Twitter, saidai hakan bai hanashi faduwa zaben fidda gwani na sanata da ya nema ba a jiharsa ta Kogi.
Akwai kuma sanata Shehu Sani;
Sanata Shehu Sani na da mabiya Miliyan 2.5 a shafinsa na Twitter sannan da wasu da dama a Facebook amma shima ya fadi zabe inda ya kare da kuri’un da basu wuce 3 ba a zaben fitar da dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar PDP.
Sai kuma tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad.

Bashir Ahmad na da mabiya Miliyan 1.1 a shafinsa na Twitter da kuma wasu da yawa a shafinsa na Facebook wanda kuma shima ya fadi takarar dan majalisa na mazabarsa inda ya kare da kuri’u 16.
Da yawan maau sharhi dai sun rika cewa siyasa ba a shafukan sada zumunta take ba.