fbpx
Friday, August 12
Shadow

‘Yan ta’adda ne suka hanamu baku wutar lantarki yanda ya kamata>>Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ‘yan ta’adda ne suka hanata baiwa ‘yan Najariya wutar lantarki yanda ya kamata.

 

Tace wannan matsala ta fi kamari a yankin Arewa maso gabas.

 

Ministan wutar lantarki, Abubakar Aliyu ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan ganawar da aka yi dashi a fadar shugaban kasa.

A zaman majalisar zartaswa ta amince da ayyukan gyaran wutar lantarki da suka kai N23,047,974,090.

 

Ya koka da cewa ‘yan Bindigar sun dukufa suna lalata kayan samar da wutar lantarki.

Leave a Reply

Your email address will not be published.