fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Yan Ta’adda Sun Fara Amfani Da Soshiyal Midiya Wajen Daukar Sabbin Membobi Domin Tayar Da Zaune Tsaye A Nijeria, Cewar Minista Sheikh Pantami

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Pantami, ya ce kungiyoyin yan ta’adda na amfani da kafofin ra’ayi da sada zumunta wajen daukan sabbin mambobi domin tayar da zaune tsaye a Najeriya.

Sheik Pantami ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake gabatar da muhadara kan yaki da ta’addanci a cibiyar NARC Abuja.
Ministan yace: “Ya bayyana karara cewa ‘yan ta’adda na amfani da soshiyar midiya wajen daukan sabbin ma’aikata domin kai hare-hare.” 
“Wannan sabon abu na bukatar hanyoyin zamani wajen kawar da ta’addancin.”
 “Hukumar Soji da hukumomin leken asiri za su iya amfani da yanar gizo wajen yakar ta’addanci.
 Za’a iya amfani da yanar gizo wajen sanin shirye-shirye da yadda wadannan kungiyoyi ke gudanar da ayyukansu.” 
Mun kawo muku rahoton cewa Ministan sadarwa, Dakta Isa ali Pantami, ya umurci hukumar sadarwan Najeriya NCC ta tabbatar da cewa kada kowani dan Najeriya ya mallaki fiye da layukan waya 3. 
Ministan ya bada umurnin ne a ranar Laraba a jawabin da hadimin, Dakta Femi Adeluyi, ya rattaba hannu inda ya umurci NCC ta sake duba dokar rijistan layukan waya. 
Jawabin ya kara da cewa akwai bukatan hakan ne bisa ga rahoton da aka samu daga hukumomin tsaro, bayan samun nasarar kawar layukan da ba’ayi rijista ba a Satumban 2019. 
Ministan ya kara cewa hukumar NCC ta tabbatar da cewa sai mutum ya mallaki lamban zama dan kasa NIN kafin ya iya rijistan layi. Wadanda kuma ba yan kasa ba, a yi amfani da bizansu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Shugaba Buhari ya nada sabuwar mai bashi shawara akan harkar siyasa


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.