fbpx
Friday, August 12
Shadow

‘Yan ta’adda sun kaiwa ‘yan mahalissar jihar Baushi hari sun ji masu rauni tare da bata masu kadarori su yayin da suke gudanar da taro

‘Yan ta’adda sun kaiwa ‘yan majalissar jihar Bauchi mummunan hari a gidan suke karbar baki yayin da suke gudanar da taro.

Inda suka fasa masu gilasan motoci da kuma tagogin gidan nasu, kuma sun kai harin ne kwana daya bayan da sukayi kokarin babbake gidan majalissar jihar.

‘Yan ta’addan su hamsin ne suka masu wannan harin kuma sun jiwa wasu daga cikin ‘yan majalissar rauni.

Daya daga cikin ‘yan majalissae ne ya bayyanawa manema labarai hakan, wato Ado Wakili kuma yace sun ji masa rauni shima.

Leave a Reply

Your email address will not be published.