fbpx
Monday, August 8
Shadow

Yan ta’adda sun kashe sojoji bakwai a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Rahotanni sun ce ‘yan ta’adda sun yi wa sojoji bakwai kwanton bauna a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa, harin ya afku ne a kusa da barikin Zuma da ke kan titin yankin Suleja a jihar Neja da sanyin safiyar Laraba 29 ga watan Maris.

Wata majiyar soji ta shaida wa jaridar cewa kwamandan ya samu kiran waya inda ya tura mutanensa wurin da lamarin ya faru.

Majiyar ta ce sabanin rade-radin da ake yi cewa an mamaye barikin an kuma kashe wasu sojoji, harin kwantan bauna ne da ke kusa da ginin.

Wani Aziz Garba da Garba M, sun raba hotunan wasu sojojin da aka ce ‘yan ta’addan sun kashe.

A wani labarin makamancin haka, Rundunar Sojan Sama na Operation Thunder Strike ta kai harin bama-bamai a wasu maboyar ‘yan ta’adda da misalin karfe 2 na yammacin ranar Laraba. Sai dai ba za a iya tantance adadin ‘yan ta’addan da aka kashe a harin ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.