Sunday, May 31
Shadow

‘Yan ta’adda sun kori sarakuna da hukumomi sun nada kansu Alkalai a yankunan mu>>Sanata Gobir me wakiltar mazabar Sokoto ta Gabas

Sanata Ibrahim Gobir dake wakiltar mazabar Sokoto ta Gabas a majalisar dattijai ya bayyana cewa ‘yan bindiga sun mamaye yankinsu inda suka kori hukumomi suka nada kansu Alkalai.

 

Ya bayyana cewa sojojin Nijar ne ke ba wasu kauyukan dake da iyaka da kasar Nijar kariya saboda idan sun kira sojojin Najeriya sai su ce musu makaman ‘yan bindigar ya fi nasu kyau.

Yace basa Noma saboda da kaje Gona suka ganka to harbinka zasu yi.

 

Ya bayyana hakane a hirar da yayi da Jaridar Punch inda ya kara da cewa abin takaici shine sun sha aikawa da bangaren zartaswa da matsaya kan a dauki mataki amma abin ya faskara.

 

A makon daya gabatane dai majalisar ta sake daukar wata matsaya inda ta bukaci bangaren zartaswa ya aika da jami’an tsaro Arewa Maso gabas dan kawar da ‘yan bindigar.

 

Saidai Gobir yace duk da Sokoton na cikin inda sojojin zasu kai dauki amma yana tunanin da wuya ta canja zani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *