‘Yan ta’adda sun kaiwa ofishin ‘yan sanda hari a Eika-Ohizenyi dake karamar hukuma Okehi a jihar Kogi.
Kuma sun saka bam a ofishin sun babbaka shi inda suka kashe wani babban insfeto a ofishin mai suna Jibril a cewar manema labarai Peoples Gazette.
Da safiyar ranar juma’a ne suka kai wannan mummunan harin da misalin karfe biyu kafin ya waye, kuma sun budewa ofishin wuta kafin sun dasa bam din.
Inda wani mazaunin yankin ya bayyanawa manema labarai cewa sun dauki tsawon awanni biyu suna gudanar da ta’addancin nasu amma ba’a kawowa ‘yan ofishin dauki ba.