‘Yan ta’addan ISWAP sun kai sabon hari jihar Borno inda suka kashe dan sanda guda daya bayan da sukayi musayar wuta a tsakaninsu.
‘Yan ta’addan sun kai harin ne ranar litinin a Aunu dake karamar hukumar Konduga wanda ke kusa da babban birnin Borno, wato Maiduguri.
Kuma sun kai masu harin ne a daidai inda suke tsayawa akan titi suka fara musayar wuta a tsakaninsu.
Inda har dan sanda guda ya mutu kuma wasu da yawa suka jigata sakamakon harbin su da aka yi.
Masani akan hare-haren ‘yan ta’adda ne ya bayyana hakan wato Zangola Makama.